Bankin Duniya ya amince, da tsarin basussuka da tallafi ga ƴan ƙasar Ukraine na kusan sama da dala biliyan bakwai.
Bankin ya ce, waɗannan kuɗaɗen za su taimaka wa gwamnatin Ukraine toshe kafofi da dama ciki har da biyan ma’aikatan asibiti da ƴan fansho da waɗanda suka manyanta da kuma tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.
Ƙasashen Sweden da Holland ne za su tsaya wa Ukraine, domin ganin wasu kuɗin sun fito, haka kuma akwai wasu tallafin kuɗi na musamman daga ƙasashe kamar Birtaniya da Denmark da Latvia da Lithuania.