Najeriya ta samu tallafin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin bunƙasa shirinta na zamantaƙewar al’ummar ƙasar gabanin cire tallafin man fetur a watan Yunin wannan shekara, a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tafiyar hawainiya.
Gwamnati ta ce za a raba kayan tallafin ne ta hanyar amfani da na’urar aika kuɗi ga ‘yan Najeriya kusan miliyan 50 ko gidaje miliyan 10, inda ta ce waɗannan mutane suna cikin mafi raunin rukunin al’umma.
Ta ce hakan na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur kan al’umma.
Bankin Duniya ya damu cewa ƙaruwar tattalin arzikin Najeriya da kashi 2.8 bai wadatar ba wajen rage sama da kashi 40 na al’ummar da ke fama da matsanancin talauci.
Najeriya da ta kasance ƙasa mafi tattalin arzikin a nahiyar Afirka, ta ware naira tiriliyan 3.36 a bana domin kashewa kan tallafin man fetur har zuwa tsakiyar shekara ta 2023 lokacin da za ta daina biya.
Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan arzikin danyen mai a Afirka amma tana shigo da man fetur daga ƙasashen waje saboda rashin aiki da matatunta na mai ke yi.