Bankin bada lamuni na duniya IMF, ya samu yarjejeniya da Ghana a kan shirin taimako na dala biliyan uku.
Sabuwar yarjejeniyar da a ka kafa a cikin karkashin yarjejeniyar mai suna Extended credit facility, za ta yi aiki na shekara uku.
A satin baya, kudin kasar Ghana mai suna cedi darajarsa ya fadi gaba da Dala.
A watannin baya, hauhawar farashin kaya ya karu da kashi 40, domin haka, kasar Ghana na matukar bukatar kudi domin gyara tattalin arzikinta.