A ranar Juma’ar da ta gabata ne tsohon hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya musanta cewa, yana da gida a Wuse, ko kuma motoci masu hana harsashi, sabanin rahotannin da ke cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) sun kai farmaki gidan sa.
Buratai, a cikin wata sanarwa, ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin shari’a, Barr. Osuagwu Ugochukwu, ya bayyana rahotannin a matsayin batanci da tatsuniyoyi, wanda aka buga domin bata masa suna.
Wata kafar yada labarai ta yanar gizo mai suna ‘Not The Guardian’ ta buga labari – ‘Exclusive: Anti-Craft Agency, ICPC’ ta bankado biliyoyin kudade da aka ware na amfani da makamai, da harsasai don yakar Boko Haram a Abuja gidan tsohon babban hafsan soji, Buratai,’ ta ruwaito cewa, an kwato Naira biliyan 1.85 daga gidan Janar din soja mai ritaya a lokacin da ICPC ta kai farmaki gidan sa.