Pep Guardiola ya ce, bai ji takaicin yadda Manchester City ta kasa daukar Harry Kane daga Tottenham a bara.
Dan wasan na Ingila, Kane, ya bayyana ya na sha’awar barin Arewacin Landan zuwa filin wasa na Etihad, amma City ta kasa shawo kan shugaban Spurs, Daniel Levy ya ba da kudi a kan ɗan wasan.
Da alama rashin daukar sabon dan wasan gaban zai iya ruguza shirin City a wannan kakar, bayan da suka sha kashi a hannun Leicester City a Community Shield da Spurs a gasar Premier a watan Agusta, a wasan da Kane ya zauna a cikin rashin tabbas kan makomarsa.