fidelitybank

Ban taba samun matsala da uban gidana ba – Osibanjo

Date:

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce, duk da bambancin addini, shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba samun matsala ba tun hawansa mulki a shekarar 2015.

Osinbajo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande ya fitar.

Ya ce, “Shugaba Buhari musulmi ne mai kishin addini kuma ni Fasto ne; dukkanmu mun yi aiki tare har tsawon shekaru kusan bakwai; Ba mu samu matsala ba,”

“Dole ne mu yi amfani da imaninmu wajen inganta zaman lafiya da wadata ga mutanenmu; ya kamata mu hada kai don ganin al’ummarmu sun ci gajiyar addini,” inji shi.

“A wasu sassan duniya, shugabannin addini sun yi amfani da addini wajen kyautata rayuwar jama’a,” a cewar Osinbajo.

A shekarar 2019, an samu rahotannin cewa, Buhari da Osinbajo sun yi takun-saka yayin da aka bukaci shugaban da ya rika neman amincewar shugaban kasa a koda yaushe, domin tafiyar da hukumomin da ke ofishin sa. Har ila yau, akwai rahotannin da ke cewa, shugaban kasar ya kori akalla 35 daga cikin sama da hadimai 80 da ke ofishin Osinbajo.

Ko da wadannan rahotannin, mataimakin shugaban kasar ya bayyana Buhari a matsayin abin koyi na shugabanci da ke daukar mutane masu bambancin addini.

Mataimakin shugaban kasar ya bukaci malaman addini da su yi amfani da imani wajen samar da zaman lafiya, tabbatar da walwala ga al’umma da kuma ci gaban al’umma.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp