fidelitybank

Ban taɓa yin nadamar ayyana Binani a matsayin gwamnan Adamawa ba – Hudu Ari

Date:

Tsohon kwamishinan zaɓen jihar Adawama, Hudu Ari – da aka sauke a baya-bayan nan bisa zargin aikata laifukan zaɓe, ya bayyana damuwarsa kan rashin ba shi dama kan zargin da ake yi masa kafin ɗaukar cire shi daga matsayinsa.

Yayin da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya yi iƙirarin cewa ya rubuta wasiƙu da dama ga hukumar zaɓen ƙasar, domin bayyana mata ainihin abin da ya sani kan zargin da ake yi masa, amma sai hukumar ta yi watsi da wasiƙun nasa.

Ya ƙara da cewa kotun – da ta saurari ƙarar zaɓe tsakanin tsohuwar ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Binani da kuma gwamnan jihar Ahmadu Fintiri – ta ƙi amincewa da shaidarsa.

A 2023 ne lokacin da ake dakon sakamakon ƙarshe a zaɓen gwamnan jihar Adamawa, kwamishinan zaɓen jihar, Hudu Ari – wanda a doka ba shi ne da alhakin faɗin sakamakon zaɓe ba – ya bayyana ‘yar takarar APC, Aishatu Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen.

Wani lamari da ya tayar da yamutsi da tashin hankali a jihar.

To sai dai Ari ya dage cewa yana da ƙwararan hujjojin da suka sanya shi ɗaukar matakin, amma ba a gayyace shi kotun domin gabatar da su ba.

Ya ce korar da aka yi masa ba ta ɓata masa rai ba, kamar rashin ba shi damar kare kansa bisan zargin da ake yi masa.

”Aikin gwamnati wani abu ne mai cike da tsari, da dokoki da ƙa’idoji, bisa doka ya kamata a saurareni. Kuma ko Ubangiji ma ai ba zai hukunta ka ba har sai ya turo maka ɗan aike, manzanni da littattafai, kuma ka saɓa”, kamar yadda ya bayyana.

Tsohon kwamishinan ya ce bai taɓa yin nadamar abin da ya aikata ba, saboda duk abin da yi a bisa doron gaskiya yake

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp