Abdulgafar Alabelewe, wakilin jaridar The Nation a Kaduna, an yi garkuwa da su kwanan nan kuma jami’an tsaron Najeriya suka ceto, a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce bai taba tunanin zai shaki iskar ‘yanci cikin mako guda ba.
A makon jiya ne aka sace Alabelewe da Abdulraheem Aodu na jaridar Blueprint tare da ‘yan uwansu daga gidajensu na daban a Kaduna.
A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, mai taimakawa na musamman kan kafafen yada labarai ga ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Alabelewe ya mika godiyarsa ga mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da tawagarsa bisa gaggauwa da suka yi.
Ya bayyana cewa aikin ceto su da ya fitar da su daga cikin daji a ranar Asabar din da ta gabata ya ba su fata a kasar da kuma kwarin gwiwa kan yadda gwamnati za ta magance matsalar garkuwa da mutane, yana mai jaddada cewa bai taba tunanin za a ceto su cikin mako guda ba.
Ya ce, “Muna godiya ga gwamnati ta dauki matakin kuma ta tabbatar da cewa an sake mu.”
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi maraba da sakin ‘yan jarida biyu mazauna Kaduna, wadanda aka yi garkuwa da su daga gidajensu da ke wajen Kaduna a karshen mako.


