Wanda ya lashe kyautar Nobel, Wole Soyinka, ya ce, bai taba amincewa da takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 ba.
Soyinka, yayin wani taron manema labarai a Legas ranar Alhamis, ya ce, bai kada kuri’a a ranar zabe a 2015 ba.
“Karya ce a ce na goyi bayan zaben Buhari,” in ji shi, ya kara da cewa, abin da ya ce, a lokacin shi ne “kada ku zabi Jonathan.”
Farfesan ya ce, babban hakkinsa ne ya zabi duk dan takarar da yake so, kuma idan mutum ya gaza, to yana da damar ya fadi hakan.