fidelitybank

Ban san da takardar da Emefiele ya fitar da dala miliyan 6.2 a matsayin kuɗin masu sanya ido na zaɓe – Boss Mustapha

Date:

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce bai san batun wata takarda ba da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, CBN, Godwin Emefiele ya yi amfani da ita wajen biyan sama da dalar Amurka 6.2 miliyan ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a ranar Talata.

Tsohon sakataren gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar mista Emefiele, ya ce a tsawon shekarun da ya yi yana rike da wannan muƙamin ba shi da masaniya kan takardar.

Kafar yaɗa labarai a cikin ƙasar, channel TV ta ce mista Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

Tsohon sakatren gwamnatin tarayyar ya kuma shaida wa kotun cewa babu ruwan gwamnatin tarayyar da biyan masu sa ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.

Mista Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari’ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.

Ana zargin tsohon shugaban na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.

Masu sa ido a babban zaben ƙasar da aka yi a shekarar 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.

dailysun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp