Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya ce bai san da kama yaran ba har sai an gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Yusuf ya bayyana haka ne a asibitin Muhammadu Buhari, inda aka tura tawagar kwararrun likitocin domin tantance lafiyar yara 76 da aka sako.
Ya nuna godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya nuna jin dadinsa ga yaran.
“Da samun labarin lamarin, nan take na umurci babban mai shari’a da kuma kwamishinan shari’a da ya dauki nauyin lamarin.
“Ina kuma mika godiyata ga duk wanda ke da hannu wajen tabbatar da dawowar kananan yara lafiya.
“Ina kuma yaba wa iyaye bisa ga addu’o’in da suka yi da kuma nuna balaga a cikin wannan mawuyacin lokaci, a lokacin da kuma bayan sakin kananan yara da abin ya shafa.
“Natsuwarsu da juriyarsu abin burgewa ne,” in ji shi.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta yi duk mai yiwuwa na dan Adam wajen hada yaran da iyayensu tare da ba su tallafin da ya kamata domin yin kananan sana’o’i.
Ya kuma jaddada mahimmancin ilimi, tare da tabbatar da cewa yaran sun koma makaranta domin bayar da gudunmawar ci gaban jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta dauki matakin mayar da kananan yaran da aka kama a kan zanga-zangar #EndBadGovernance.