Tsohon gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya karyata rahotannin sauya shekar sa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Da yake magana a wajen fadada taron zartaswar jam’iyyar PDP, a ranar Litinin, Ortom ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar ne.
A cewar Ortom: “Rade-radin cewa zan sauya sheka zuwa APC, ba zan je ko’ina ba; wannan da suke kirana da shugaban jam’iyyar a jihar mai dimbin nauyi, ba zan bar wa kowa ba.
“APC ba ta gayyace ni ba. Ni ba mai shagaltuwa ba ne da za a yi hijira daga wannan wuri zuwa wancan, na jajirce zuwa jam’iyya ta (PDP). Wajibi ne mu mutunta jam’iyya a kowane lokaci. Mu yi dabarar komawa mulki. Yanzu ne lokacin da za mu tsara, dole ne mu tsara gaba da su kamar yadda suka yi a 2023. ”
Ortom ya kuma yi watsi da ikirarin samun sabani da tsohon gwamna Gabriel Suswam da Sanata Abba Moro.
“PDP ce kawai jam’iyyar da ke da karfi da kuma karbuwar bukatun jama’a. Da sabon alkawarin da muka yi, za mu sa jam’iyyar ta kara zage damtse a gobe.
“Za mu yi nasara a zabuka masu zuwa. Ba ni da wani sabani da Moro da Suswam, ”in ji shi.