fidelitybank

Ban kama magoya bayan Atiku ba – Wike

Date:

Gwamnatin jihar Ribas ta musanta cewa, ta damke mambobin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar su 30 a Fatakwal.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, da gwamnan Rivers, sun shiga takun saka tun bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa, ‘yan sanda dauke da makamai sun cafke kusan mambobin kungiyar yakin neman zaben su 30 a wani taro a Fatakwal.

Karanta Wannana: Wike ya zama matsoraci ya kasa bayyana dan takara – Dakuku

Kakakin kungiyar kamfen, Victor Moses, ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama shugabannin kungiyar ne na jiha da na kananan hukumomi.

Kakakin yakin neman zaben ya yi zargin cewa jami’an ‘yan sanda sun yi aiki da umarnin Wike, wanda ya sha alwashin yin aiki da Atiku a zabe mai zuwa.

Sai dai kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Chris Finebone, yayin da yake mayar da martani kan wannan zargi a ranar Litinin, ya ce rashin hankali ne kungiyar yakin neman zaben Atiku ta alakanta Gwamna Wike da batutuwan da suke da ita da ‘yan sanda.

Da yake musanta rahoton, Finebone ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa zargin na daya daga cikin abubuwan da mutane ke ganin ya dace su nuna yatsa ga gwamnatin da ke mulki.

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp