fidelitybank

Ban ji daɗin ɓarkewar faɗan Sudan ba – Buhari

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana fadan da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da rundunar masu sanye da kayan sarki ta RSF a Sudan da cewa abin damu wa ne matuka.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da shugaban gwamnatin mulkin soji na ƙasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Déby ya kai masa ziyara a Makkah da ke Saudiyya a ranar Lahadi.

Buhari ya nuna takaici kan irin asarar rayuka da ake ci gaba da samu sakamakon rikicin.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batun rikicin na Sudan, inda suka yi kira ga dukkan ƙasashe makwaɓta da kuma al’ummomin waje da su shiga tsakani domin dakatar da faɗan.

“Lamarin da ke faruwa a Sudan abin takaici ne. Sudan ta cancanci zaman lafiya idan aka duba halin da ta shiga a baya,” in ji Buhari.

Buhari ya kuma yaba wa shugaban na Chadi kan irin kokari da yake yi na ganin hankali ya kwanta a Sudan da kuma samun zaman lafiya.

Deby-Itno ya faɗa wa shugaba Buhari cewa abin da ke faruwa a Sudan abin damuwa ne wanda idan ba a ɗauki matakin shawo kan shi ba, zai iya yin mummunar tasiri kan ƙasashe makwaɓta.

Shugaban na Chadi ya ce cikin irin matakai da ƙasarsa ta ɗauka kan rikicin, sun haɗa rufe iyaƙar ƙasar da Sudan da ƙara karfafa matakan tsaro.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp