Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya musanta rahotannin da ke cewa, ya bayyana goyon bayan sa ga shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan na takarar shugaban kasa a jamâiyyar All Progressives Congress (APC).
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa guda biyu daban-daban daga masu taimaka masa kan harkokin yada labarai, Uchenna Orji da Francis Nwaze.
Ya na mai da martani ne kan rahotannin da ke cewa, ya janyewa Lawan takarar shugaban kasa, wanda ya ziyarce shi ranar Asabar a gidan gwamnan Abuja.
Mista Umahi ya kuma wallafa hotunan ziyarar a shafukan sa na sada zumunta da aka tabbatar.
âAbin farin ciki ne na tarbi dan uwana, abokina kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan tare da tawagarsa wadanda suka hada da Sanatoci shida zuwa gidana na Abuja a baya-bayan nan,â Gwamnan Ebonyi ya rubuta a shafinsa na Facebook.