Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa, ya janye takarar shugaban kasa gabanin zaben fidda gwani na jamâiyyar All Progressives Congress (APC) da za a yi ranar Litinin.
Osinbajo ya bayyana haka ne a wata sanarwa da shugaban kwamitin yakin neman zaben sa, Richard Akinnola II ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Akinnola yayin da yake karyata rahoton ya ce masu yada labaran karya âsuna tsoron babbar goyon bayan siyasa na mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.â
Sai dai ya ce Osinbajo ba ya tunanin sauka daga mulki ga kowa, yana mai jaddada cewa mataimakin shugaban kasa a shirye yake don zaben fidda gwani kuma yana da tabbacin samun nasara.
Majalisar ta kuma yi maraba da dukkan wakilan da ke shigowa babban birnin kasar nan domin gudanar da zabukan fidda gwani na jamâiyyar APC da aka shirya yi a ranakun Litinin da Talata.
A wani bangare sanarwar ta ce, âsuna maraba da manyan wakilanmu daga sassan kasar nan zuwa Abuja domin gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa.