Biyo bayan bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewa, dukkan masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC su hadu su fito da wani babban dan takara, tsohon ministan Neja Delta kuma daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki, Godswill Akpabio, ya ce bai janye daga neman kujearar ba.
Tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, wanda ya yi watsi da ikirarin janyewar da ya yi a shafukan sada zumunta a matsayin mugunyar karya, ya bayyana matsayinsa a wani sako da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi.
Ya bukaci wakilan da su yi watsi da wannan ikirari, yana mai kira da a ba su cikakken goyon baya a zaben fidda gwani na shugaban kasa a ranar Litinin. In ji Ripple Nigeria.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ya ku wakilai na kasa, don Allah ku yi watsi da karyar da ke zagayewa, zabinku na ofishin Shugaban Tarayyar Najeriya a 2023, na janye daga takarar.