Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa a ranar Laraba ya bayyana cewa rashin kammala zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata bai damu ba, domin Allah zai sa al’ummar jihar su fito su zabe shi.
Fintiri, wanda ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC.
Ya ce, “muna jiran lokacin da za a kammala zabe a bayyana wanda ya yi nasara.
“A wannan karon, Allah zai maimaita tarihi a gare ni. Jama’ar Adamawa za su yanke shawara su zabe ni da gagarumin rinjaye. Na tabbata zan sami kuri’u masu rinjaye da yardar Allah.
“Ban damu ba, na yi imani da Allah Madaukakin Sarki, wanda zai tabbatar da lokacin da ya dace da za a sanar da ni nasara.”
Gwamnan da ake ci gaba da dakon sakamakonsa, ana sa ran zai fitar da Fintiri, wanda kuma zai kasance gwamna mai ci ko kuma Aishatu Ahmed Binani ta jam’iyyar APC, wacce a halin yanzu ke wakiltar Adamawa ta Arewa.
Sakamakon da aka gani ya zuwa yanzu ya nuna cewa dukkansu Fintiri da Binani ne ke kan gaba.