fidelitybank

Ban aikata wani laifi ba har da EFCC za su kai min ziyara – EFCC

Date:

Rukunin kamfanin Dangote, ya ce, bai aikata wani laifi, ko ba daidai ba da ya sa jami’an hukumar EFCC mai yaĆ™i da cin hanci da rashawa suka ziyarci babban ofishinsa ba.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar kan ziyarar da jami’an hukumar suka kai babban ofishinsa da ke Legas ranar 4 ga watan Janairu, ya ce ya fahimci girman damuwa da maganganu da hakan ya janyo tsakanin abokan hulÉ—arsa, da sauran mutane, don haka ne ma kamfanin ya ce ya fitar da sanarwar don fayyace ainihin abin da ya faru.

Sanarwar ta ce a ranar 6 ga watan Disamban 2023, ya samu wasiƙa daga Babban Bankin ƙasar, CBN, inda aka buƙaci kamfanin ya bayar da bayanan canjin kuɗin ƙasar waje da CBN ɗin ya bai wa kamfanin tun daga shekarar 2014 zuwa yau.

Kamfanin ya ce ya kuma rubuta wa hukumar EFCC takardar da ke nuna cewa kamfanin ya karɓi takardar buƙatar bayar da bayanan da aka buƙata.

”Mun kuma buĆ™aci Ć™arin lokaci domin kammala tattara bayanan, don gabatar da su kamar yadda aka buĆ™ata kasancewa bayanan shekara 10 aka buĆ™ata”, in ji sanarwar.

To amma kamfanin ya ce hukumar EFCC ba ta ba shi amsa kan buƙatar ƙarin lokacin da ya nema ba, sannan bai ƙara musu lokacin ba, a maimakon haka sai ya dage cewa sai kamfanin ya gabatar da takardun bayanan da aka buƙace shi a lokacin da aka buƙata.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk da ƙurewar lokacin da ya fuskanta, ya tabbatar wa da hukumar EFCCn aniyarsa na gabatar da takardun amma ya alƙawarta gabatar da takardun rukuni-rukuni.

Kamfanin ya ce a ranar 4 ga watan Janairun 2024, wakilansa suka gabatar da rukunin farko na takardun ga hukumar EFCC, amma sai jami’an na EFCC suka ki karÉ“ar takardun, suka dage cewa sai sun ziyarci babban ofishinsa domin karÉ“ar takardun da hannunsu.

”A yayin da wakilan kamfaninmu ke ofishin EFCC don gabatar da takardun, sai ga jami’an hukumar a ofishinmu da nufin karÉ“ar takardun da an riga an kai musu ofishinsu, sun zo a wani yanayi da ba mu ji daÉ—insa ba, domin hakan tamkar wulaĆ™anta mu ne” kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Abin takaicin ma shi ne jami’an ba su karÉ“i takardun a babban ofishin namu ba lokacin ziyarar tasu, kasancewar tuni takardun na ofishinsu”.

Kamfanin ya ce a matsayinsa na wanda ke bin doka da oda, a kodayaushe a shirye yake ya baiwa hukumar ta EFCC haÉ—in kai bisa duka bayanan da take nema.

”Tuni mun bai wa hukumar rukunin farko na takardun da take buĆ™ata, kuma muna aiki wajen tattara rukuni na biyu domin bai wa hukumar a kan lokaci domin gudanar da aikinta”.

Kamfanin na Dangote ya ce – a matsayinsa na É—aya daga cikin masu taimaka wa tattalin arzikin Najeriya, kuma babban kamfanin da ya fi É—aukar ‘yan Najeriya aiki, wanda kuma ya kasance É—aya daga cikin mayan masu biyan haraji a Ć™asar – a kodayaushe shi mai bin doka da oda ne, kuma a shirye yake wajen yin duk wani abu da zai taimaka wajen mayar da Ć™asar mai kyakkyawan yanayin zuba jari ga ‘yan Ć™asar da na Ć™etare.

dailypostnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar Ć´an Ć™asarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp