Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Cross River, Sanata Sandy Onor, ya bayyana cewa jam’iyyar sa ta yi addu’a, sakamakon tikitin da Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya samu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Da yake bayyana hakan a lokacin da yake magana a wani taron manema labarai a Calabar, babban birnin jihar, Onor, ya ce, jam’iyyar PDP ta yi fatan rashin nasarar Tinubu a zaben, domin samun sauki a zaben shugaban kasa na 2023 ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsu, Alhaji Atiku Abubakar.
“Fitowar Tinubu shine abin da ba mu so ya faru ba. Amma ko ta yaya APC ta shawarci kanta kuma sun kawo shi,” inji Onor.
Onor ya ce, zaben shugaban kasa zai kasance mai tsauri tsakanin Tinubu na APC da Atiku na PDP, kuma wadanda suka zaba a matsayin mataimaka za su yi tasiri da shawarar da masu zabe za su yanke.
Onor ya bukaci wadanda suka kai shekarun yin kuri’a da su fito su yi rajista, domin su samu damar kada kuri’a a babban zaben 2023.