Sanusi Garba, Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya NERC, ya ce, hukumar ba ta amince da wani sabon karin farashin sabon kudin lantarki ba a ‘yan kwanakin nan.
Garba ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a cewa an amince da sake duba kudin fito na karshe a ranar 31 ga Disamba, 2021, kuma ya fara aiki a watan Fabrairun 2022.
“Ina so a madadin hukumar NERC, in bayyana karara cewa ya zuwa yau, ba mu amince da sake kara duba farashin kudi ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa, duk wani Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) na kara farashin sa. A cewar Daily Nigeria.