fidelitybank

Bamu kama maharan da suka kai hari Cocin Owo ba – ‘Yan sanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta musanta rahotannin da ke cewa, ta kama maharan da suka kashe masu ibada fiye da 40 a harin da suka kai Cocin Katolika ta St. Francis a jihar.

Rahotannin da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta sun bayyana cewa, dakarun haɗin gwiwa na sojoji ne da ‘yan sanda da na rundunar Amotekun suka kama maharan a ranar Alhamis.

Sannan sun yi iƙirarin cewa an kai mutanen fadar Mai Martaba Olowo na Owo Oba Ajibade Ogunoye, inda mutane suka yi tururuwa don ganin waɗanda ake zargin.

Sai dai basaraken ya musanta batun kamen yayin hirarsa da jaridar Punch a yau Juma’a. “Rahoton ba gaskiya ba ne,” in ji shi. “Mutane sun yi ta zuwa fada don ganin su amma Olowo ya faɗa musu babu wanda aka kawo fadar.”

Ita ma kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce babu wanda aka kama da zargin kai harin na ranar Lahadi da ta wuce.

Gwamnatin Najeriya ta ce ƙungiyar ISWAP mai alaƙa da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Islamic State (IS) ce ta kai harin. In ji BBC.

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp