Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana harin jirgi maras matuƙi na baya-bayan nan da aka kai jihar Kaduna wanda ya halaka mutum kusan 100 a matsayin abin tashin hankali da ba a buƙatar faruwarsa.
A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, an kai harin ne sakamakon bayanan sirrin da aka samu cewa akwai ƴan bindiga a yankin.
Harin dai ya faru ne dai-dai lokacin da mutane a ƙauyen Tudun Biri suke gudanar da taron bikin Mauludi.
Tuni dai gwamnan jihar ta Kaduna, Uba Sani ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin da ya jikkata wasu gommai.
Rundunar sojin ƙasar ta ce lokaci zuwa lokaci ta kan ƙaddamar da irin wannan hari kan ƴan bindiga da a wani lokacin yake shafar al’ummar gari.
Zuwa yanzu, waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitin gwamnati a jihar.
Jihar Kaduna na fama da matsalar tsaro inda tsawon shekaru, ƴan bindiga ke kai hare-hare tare da yin garkuwa da jama’a don neman kuɗin fansa.


