fidelitybank

Bam ya tashi a yankin shugaban majalisar dattijai

Date:

An sami fashewar wani abu daddare wanda ya haddasa tashin hankali a garin Gashua na jihar Yobe.

Al’ummar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya fito sun shiga cikin fargaba a daren Lahadi, bayan da wata na’urar da ba a tantance ba ta fashe, inji rahoton Naija News Hausa.

Gashua na cikin karamar hukumar Bade, kimanin kilomita 188 daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Fashewar daren Lahadi a cewar rahotanni, ya afku ne a wani wurin shan giya da ke unguwar Abasha a garin a lokacin da musulmin ke gudanar da sallar magariba.

Wani mazaunin al’ummar da ya shaida wa Daily Post, ya ce suna Sallah ne a masallatai da misalin karfe 8 na dare, sai suka ji karar fashewar bam din da ake zargin bama-bamai ne.

Rahotanni sun ce mutum daya ya mutu a lamarin yayin da wasu akalla bakwai suka samu raunuka daban-daban.

Nan take aka garzaya da su Asibitin Kwararru da ke Gashua domin jinya, kamar yadda majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp