Akalla mutum hudu ne suka mutu sakamakon bam din da aka tasa a kusa da wani masallaci da ke birnin Kabul na Afghanistan.
Kafar yada labaran yankin ta rawaito, an jefa bam din ne kusa da masallacin Wazir Akbar Khan, jim kadan bayan an sauko daga sallar juma’a a yau.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Kuma yana zuwa ne wata guda bayan an kai irinsa a wani masallaci duk dai a birnin Kabul, inda mutum 20 suka mutu.