Dan wasan bayan Queen Parks Rangers, Leon Balogun, ba zai buga sauran wasannin kakar bana ba saboda rauni.
Balogun dai ya sha fama da rauni tun lokacin da ya koma kungiyar ta Landan kan cinikin kyauta a bazarar da ta gabata.
Kwanan nan dan wasan na Najeriya ya dawo taka leda a QPR bayan ya shafe kusan watanni hudu yana jinya saboda rauni.
Kocin QPR, Gareth Ainsworth ya bayyana cewa dan wasan na baya ya sake samun rauni wanda zai hana shi jinya har tsawon kakar wasa ta bana.
“Ossie Kakay da Leon Balogun ne kawai za su yi jinya a sauran kakar wasanni kuma na ji dadi saboda su duka kwararru ne,” in ji Ainsworth a wani taron manema labarai.
Dan wasan bayan ya buga wa QPR wasanni 12 a kakar wasa ta bana da kwallo daya.