Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulƙadir Kauran Bauchi na jam’iyyar PDP ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya ce Bala Ƙaura ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280.
Ya doke babban abokin hamayyarsa Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 432,272.
Jihar Bauchi dai na ɗaya daga cikin jihohin da fafatawa ta yi zafi a zaɓen gwamnonin a Najeriya.