Sama da baki 2000 ne daga kasashe daban-daban a fadin duniya, ake sa ran za su halarci jana’izar Sarauniyar Ingila Elizabeth ll.
A lokacin gudanar da jana’aizar za a yi shiru na minti biyu.
A yanzu dai an bude kofofin dakin taro na Westminster Abbey a shirye-shiryen jana’izar da za a gudanar ranar Litinin 19 ga watan Satumba. A cewar BBC.