Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya taya ƴanmatan nan uku da suka nuna bajinta a wata gasa ta TeenEagle da aka yi a Birtaniya.
Ƴanmatan Nafisa Abdullahi mai shekara 17 ta haskaka a gasar Turanci yayin da Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15 ta fi kowa hazaƙa a muhawara da Hadiza Kashim Kalli ta lashe kyautar mafi fiƙira.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yaba wa matasan ƴan Najeriyar saboda bajintar da suka nuna a gasar .
Ya kuma yaba wa makarantu da sauran cibiyoyin karatu inda ya ce irin waɗannan nasarori na bayyana yanayin ingancin da ilimi ke da shi a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana ilimi a matsayin tushen duk wani ci gaban ƙasa, abin da ya sa ma a cewarsa gwamnatinsa ke fifita ɓangaren tare da ganin ta kawar da duk wata matsala ta kuɗi da za ta hana ƴan ƙasar ci gaba da karatu ta hanysar tsarin tallafin karatu na NELFUND.
Shugaban ƙasar ya kuma ƙarfafa wa Nafisa da Rukayya da Hadiza gwiwar mayar da hankali a karatu tare da yi masu fatan samun ƙarin nasarori a rayuwarsu.