Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce, ba zai yiwu a baiwa Ukraine matsayin gurbin takarar Tarayyar Turai ba, idan ba don mamayewar Rasha ba.
Macron ya gaya wa CNN da BFMTV ranar Juma’a cew,a “Kada a ce Ukraine ba ta zama dan takara ba” kuma “suna yin hakan ne saboda yakin kuma saboda muna ganin yana da kyau.”
Ya bayyana hakan ne a cikin wani jirgin kasa da ya tashi daga Ukraine bayan ziyararsa a Kyiv, inda ya kasance memba na tawagar kasashen Turai don kwantar da tarzoma kan abin da jami’an Ukraine suka dauka a matsayin goyon bayan da suke yi na kare kai daga Rasha.
Shugaban na Faransa ya ce “alama ce, sako ne ga Ukraine ta ce suna cikin dangin Turai.”
Yayin da Macron ya ce, yawancin yammacin Turai na goyon bayan shirin, “muna da kasashen da suka fi jajircewa,” in ji shi.
Shugaban na Faransa ya kara da cewa za a yanke shawara kan batun takarar Ukraine a kungiyar EU a taron majalisar Turai a ranar Alhamis da Juma’a mai zuwa.