fidelitybank

Bai kamata Kwankwaso ya rinka yin magana sakaka ba – APC

Date:

Jamiyyar APC mai mulki ta ce bai kamata tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya riƙa yin kalamai sakaka, ba tare da kame baki da lura da abin da zai iya haifarwa a kan lamarin jihar Kano ba.

Jam’iyyar ta ce a matsayin Kwankwaso na dattijo a ƙasa kamata ya yi ya mayar da hankalinsa kan lalubo duk wata hanya ta siyasa da lumana don magance rikicin masarautar jihar maimakon rura wutar dambarwar.

Kiran na kunshe ne a martanin da jam’iyyar ta APC ta mayar wa da Kwankwason, mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa Felix Morka, kan zargin da tsohon ɗan takarar ya yi cewa gwamnatin APCn, na neman haddasa rigima a jihar ta Kano, domin a kai ga kafa dokar ta-ɓaci ta yadda za ta yi amfani da hakan domin karbe jihar.

A lokacin ƙaddamar da wani aiki da gwamnatin jihar ta yi ne, Sanata Rabi’u Musa Kwankwason ya yi zargin cewa wasu sun hada baki da jagororin jam’iyyar APC suna kokarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da rikici, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci.

Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin wanda ba shi da tushe.

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta nesanta shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da duk wani yunƙuri na haddasa rikici a duk wani sashe na kasar da yake shugabanta, tana mai cewa a matsayinsa na jagoran jam’iyyar kuma mai kishin ƙasar a dunƙule, bai kamata kai tsaye ko a fakaice a ɓata masa suna da zargin neman haddasa fitina ba a ko’ina a ƙasar.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp