Shugaban Kwamitin amintattu na babbar jam’iyyar adawa, PDP, Walid Jibrin, ya ce, bai kamata a ce shugaban jam’iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar su fito daga arewacin kasar ba.
Walid Jibrin ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV.
Jibrin ya ce dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, dukkansu daga arewacin kasar suka fito inda ya ce hakan ba daidai ba ne.
Ya ce “A hakikanin gaskiya bai dace a ce da shugaban jam’iyya da dan takarar shugaban kasa na jam’iyya da kuma shugaban kwamitin amintattu na jam’iyya duk su fito daga yanki guda ba. Abin da ya kamata mu yi shi ne mu yi abin da ya dace da muradin jam’iyya ba son rai ba.”
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, wanda ya ce bai damu ya sauka daga mukamin nasa ba don ci gaban jam’iyyar, ya kara da cewa jam’iiyarsu ce za ta samu nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Kalaman Walid Jibrin na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da rikici a jam’iyyar ta PDP, tun bayan tsayar da Atiku Abubakar a matsayin wanda zai tsaya wa jam’iyyar takarar shugaban kasa.


