fidelitybank

Bai kamata a rinka yin zabe daban-daban a Najeriya ba – Jonathan

Date:

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, ya nemi majalisar tarayyar ƙasar ta mayar da lokutan zaɓen gwamna lokaci ɗaya a ƙasar ba tare da ware wasu ba kamar yadda ake yi a yanzu.

Jonathan ya yi kiran ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da ke gudana a yau Asabar tare da na jihohin Kogi da Imo.

“Idan muka ci gaba da yin irin wannan zaɓen na bayan babban zaɓe saboda shari’o’i to wata rana shi ma zaɓen shugaban ƙasar Najeriya zai sauka daga lokacin da aka saba yin sa,” in ji shi.

Ya bayar da misali da zaɓen shugaban ƙasa na 2007, inda ya ce alƙalan kotun ƙoli uku cikin bakwai ne suka ce a sake zaɓe, yayin da huɗu suka amince da sahihancinsa.

“Da a ce alƙali ɗaya ya bi sawun waɗanda suka ce a sake zaɓe da tuni zaɓen shugaban ƙasa ya sauka daga kan lokacin da aka saba yin sa.”

Jihohin sun sauka daga layin lokacin da aka saba gudanar da babban zaɓe ne saboda hukunce-hukuncen kotu da ke ƙwacewa ko kuma su bayar da umarnin a sake zaɓe a jihohin.

Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da saura a Najeriya, waɗanda suka haɗa da Kogi, da Imo, da Bayelsa, da Edo, da Anambra, da Osun, da Ekiti.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp