fidelitybank

Bai kamata a dauki aikin Soja a matsayin sana’ar samun kudi ba – Laftanar Farouk

Date:

Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Forouk Yahaya, ya ce, bai kamata a ɗauki aikin soja a matsayin sana’ar samun kuɗi ba kamar sauran sana’o’i.

Janar Yahaya ya bayyana haka ne bayan da ya ziyarci sansanin tantance sabbin sojojin da rundunar sojin ƙasar za ta ɗauka aiki a cibiyar tantance lafiya da cancantar soji da ke dajin Falgore a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Yayin da yake bayyana matsayarsa, babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar ya ce saɓanin sauran sana’o’i, shi aikin soji amsa kira ne domin tsaron ƙasa, dan haka ake buƙatar ‘yan ƙasar masu cikakkiyar lafiyar gaɓɓai da ƙwaƙwale tare da fikira.

Ya ƙara da cewa shiga aikin soji ba sana’a ce ta samun kuɗi ba, a maimakon haka aiki ne na hidimta wa ƙasa, dan haka yake buƙatar sadaukarwa, da jajircewa da kuma juriya, domin kuwa ba aiki ne na gama-garin mutane ba.

Babban hafsan sojin ƙasan ya shawarci matasan da ake tantancewar da su maida hankali domin kuwa waɗanda suka nuna ƙwazo ne kaɗai za su samu nasarar tsallake matakin tantancewar.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp