Wasu shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewacin Najeriya ke cigaba da ƙara ƙaimi wajen ganin an samar da haɗin kai tsakanin al’ummomin yankin.
Shugaban kwamitin amintattu na sabuwar ƙungiyar, wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC cewa manufar ƙungiyar shi ne hadin kai da amincewa da juna.
Ya ce sabuwar ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, kuma babu ruwanta da siyasa.
”Ƙungiya ce ta haɗin kan mutanen Arewa, da wayar da kan ƴan yankin su daina bari ana amfani da su wajen cimma muradun siyasa”, a cewar Bafarawa.
Akwai ƙungiyoyi da dama dai aka kafa da nufin kare muradun ƴan arewa, to sai dai wasu na ganin babu wani tasiri da ƙungiyoyin ke yi.