Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya haramta amfani da motoci da babura da sauran nau’o’in gangamin murnar lashe zaben gwamnan jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Habibu Nuhu Kila ya sanyawa hannu.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomi ashirin daga cikin ashirin da bakwai na jihar.
A wani sako na musamman ga al’ummar jihar, Gwamnan ya bukaci jama’a da su kwantar da hankula da kuma da’a idan aka bayyana wanda ya yi nasara.
Alh Muhd Badaru Abubakar yace Allah ne ke bayarwa kuma ya kwace mulki don haka kowa ya zama mai godiya da godiya ga Allah.
Ya bayyana godiya ga al’ummar jihar bisa yadda aka gudanar da zaben cikin lumana da nasara a fadin jihar