Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya ƙara zurfi, bayan an gano cewa Kwamishinan Raya Karkara, Abdulkadir Abdulsalam, ya amince da biyan kuɗi ₦1.17 biliyan a matsayin kuɗin kwangilar bogi.
Abdulsalam, wanda a lokacin yake rike da mukamin Akanta Janar na jihar, ya amsa wannan batu a gaban jami’an Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) lokacin da aka yi masa tambayoyi.
Tushen Almundahana:
Binciken ICPC ya nuna cewa wannan biyan kuɗi ya zama asalin wani shirin almundahana da ya kai kimanin ₦6.5 biliyan. An zargi Abdulsalam da haɗin baki da Abdullahi Rogo, Daraktan Al’amuran Gwamna Abba Kabir Yusuf, wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati ta hannun ‘yan canji (BDC operators).
Takardun Bogi:
ICPC ta gano cewa an yi amfani da takardun bogi da aka ɗora wa sunayen kamfanonin A.Y. Mai Kifi Oil and Gas Ltd. da Ammas Petroleum Company Ltd. Shugabannin kamfanonin biyu sun shaida wa masu bincike cewa an tilasta musu sanya hannu bisa umarnin tsohon Akanta Janar.
Yadda Aka Yi Karkatar Kuɗin:
Rahotanni sun nuna cewa a ranar 9 ga Nuwamba 2023, an fitar da ₦1.17 biliyan daga asusun FAAC na Kano aka tura ga ‘yan canji Gali Muhammad (Kazo Nazo) da Nasiru Adamu (Namu Nakune).
Daga nan aka mika dala $1 miliyan a hannu ga Abdullahi Rogo a ofishin Kano Liaison da ke Asokoro, Abuja.
Martanin ICPC:
Hukumar ta bayyana cewa Abdulsalam da Rogo sun yi hadin baki wajen fitar da kuɗin gwamnati ta kasuwar canji. A halin yanzu, ICPC ta samu nasarar dawo da ₦1.1 biliyan daga cikin kuɗin da aka karkatar.
Sai dai duk da ya amince da bayar da izinin biyan kuɗin, Abdulsalam bai iya bayyana dalilin da ya sa aka karkatar da kuɗin zuwa hannun ‘yan canji ba. Haka kuma bai amsa kiran waya da saƙonnin da PREMIUM TIMES ta aika masa ba.