fidelitybank

Badakalar Kudi: Gwamnan Zamfara da mataimakin sa sun dau zafi

Date:

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da mataimakinsa, Barista Mahdi Gusau, sun fara musayar yawu kan karkatar da kuɗaɗen al’ummar jihar da ake zargi.

Daily Trust ta rawaito cewa, Sakataren mataimakin gwamna, Aminu Umar, ya kalubalanci Matawalle ya fito ya yi wa al’umma jawabin yadda ya kashe Naira biliyan 31, waɗan da ya karba a watanni 31.

Umar ya bukaci gwamnan ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya tafiyar da kuɗaɗen da aka ware masa na tsaro, kasafin Ofishinsa, Sakatarensa, da kuma gidan gwamnati tun da ya hau mulki.

Ya ce, tun farkon kafa gwamnati, gwamna na karbar Naira miliyan 600 na tsaro duk wata, miliyan 350 tsabar kuɗin Ofishinsa, Miliyan 30 na ofishin PPS da kuma miliyan 30 na kasafin fadar gwamnati. Wadna kuɗin sun kama Naira Biliyan 1.1 duk wata, wanda idan ka nunka sau 31, kuɗin sun zama Biliyan 31.3.

Sai  dai da yake martani kan maganar, kakakin gwamna Bello Matawalle, Zailani Bappa, ya yi fatali da zargin, inda ya ce, farfaganda ce kawai suke yi, domin  kuwa idan suna da kwakkwarar hujja su rubuta korafi kan mai girma gwamna su gabatar wa hukumomin dake da alhaki. Wannan zancen na su na nuna cewa, kasala ta hana su gano gaskiya. Uban gidansu na daga cikin waɗan da suka tafiyar da harkokin gwamnati na shekaru biyu da rabi, me ya sa ba su bankado lamarin ba tun a baya?.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp