Wani kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ce, bai da masaniya kan wani tsagaita buɗe wuta a kudancin Gaza, bayan da kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito majiyoyin tsaron Masar na cewa za a tsagaita buɗe wuta a daidai lokacin da za a bude kan iyakar Masar da Gaza.
Kakakin rundunar tsaron Isra’ila Laftanar Kanar Richard Hecht ya shaida wa BBC cewa: “Babu wata yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka amince da ita. Ina ganin duk wadannan rahotannin kuma babu wani abu da na tabbatar.”


