Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa , ya ce a yanzu babu wata hamayya da ta rage a fagen siyasar Najeriya.
A tattaunawarsa da BBC ya ce ‘yan siyasar kasar su ne ke hamayya da kansu da cutar juna game da neman mukamai ba tare da sun anfana wa talakawa wani abu ba.
Bafarawa ya bayyana hakan ne ganin yadda wasu jiga-jigan jam’iyyun hamayya na kasar ke tururuwa suna komawa jam’iyya mai mulki ta APC a wannan tsakanin yayin da ya rage wajen shekara biyu a yi babban zabe na gaba, a 2027.
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa duk wannan sauya sheka da ‘yansiyasar na bangaren hamayya ke yi suna tafiya jam’iyya mai mulki ba don komai suke yi ba na amfanin talaka, face don kansu suke yi, saboda haka ya ce siyasar hamayya ta mace a kasar a yanzu – babu akida.
”Saboda haka cikin duhu ake da mai nema da wanda ake nema, shi mai nema idonshi sun rufe ba imani ba tausayi shi dai ya samu mukami, shi kuma talaka idonshi sun rufe ga yunwa ga talauci ga jahilci saboda haka duk a yamutse ake,” in ji shi.
Alhaji Attahiru ya ce, ”adawa da ake adawa kowa kanshi yake adawa, me zai samu in ya ga waccan kofar ta rufe bai jin kunya bai jin tsoro hanyar nan da ya bata, ya bace ta nan zai sake daowa.”
”Ba wata adawa da ake yanzu kowa adawar da yake yi me zai samu, da zarar ya samu babu adawa shi talaka sai dai ya yi ta kanshi,” ya ce.
Ya kara da cewa abin takaici za ka ga ‘yansiyasar ana ta fada da juna amma ba don talaka suke yi ba sai dai don mukami, kuma mukamin da suke fadan a kai sun taba rike shi amma me suka yi da suka rike da a yanzu suke fada don su sake samunshi?
”Yanzu da kake son sake rike mukamin me ka yi wanda ba ka yi a baya ba, wanda zai sa Arewa ta ci gaba?”
Dansiyasar ya ce yankin Arewa yana cikin wani mawuyacin hali na koma-baya.
Ya ce duk inda ka ci mutum da yakin ilimi ka jefa masa jahilci to ka gama da shi.
”Yanzu mu nan dama-dama gare mu yaranmu kashi 70 cikin dari wallahi ba su da ilimi. To ta yaya kasa ko yanki za su ci gaba ba ilimi?” Ya ce.
Ya kara da cewa, ”sai ka ga shin su talakawan ga da ake wa magana sun san ciwon kansu koko mene ne?”
”Sa’annan su ‘yansiyasar da ke son su ja talakawa da gaske suke yi tsakani da Allah Suke yi?”