Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce, babu wata gwamnati da za ta iya samar da abinci ga daukacin al’ummarta.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake sa ido kan rabon kayan abinci ga magidanta 18,000 a karamar hukumar Damboa ranar Litinin.
Zulum ya lura cewa gwamnatin sa ta tantance tare da zabo ’yan kasa mafiya rauni don zama wadanda za su ci gajiyar tallafin cire tallafin don taimakawa wajen dakile illar wahala a jihar.
“Ina so ku lura cewa ba zai taba yiwuwa wata gwamnati ba, gwamnatin tarayya, jiha ko karamar hukuma, ta samar da kayan abinci ga daukacin al’ummarta.
“Bayan haka ne muka zabo wadanda suka fi kowa rauni a fadin kananan hukumomi domin su taimaka wajen dakile matsalar, Gwoza da Damboa da ke kudancin Borno suna fama da matsalar karancin abinci, kuma a yankin Arewa kusan dukkanin kananan hukumomin na fama da karancin abinci. daga Kaga, Magumeri da Gubio, yayin da a tsakiya, MMC da Jere ba su da yawa,” in ji shi.


