Gwamnatin tarayya ta bakin ministan zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa, Hadi Sirika, ya ce, babu wata doka a Najeriya da za ta hana gwamnati kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Nigerian Air
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Legas ce ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da ƙudurin samar da kamfanin jiragen sama na Nigerian Air
Hukuncin na zuwa ne bayan da wasu kamfannonin jiragen sama na cikin gida suka shigar da ƙara suna kalubalantar kafuwar kamfanin Nigeria Air, ta hanyar haɗin gwiwwa da Ethiopian Airlines.
A umarnin da kotun ta bayar ranar Talata ta ce gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da wannan yarjejeniya har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron karar domin yanke hukunci.