Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar nan cewa, babu wasu mutane ko wata ƙungiya da ke yin tasiri a sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasar.
Shugaban ya kuma jaddada cewa shi ne ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensa da kansa ba tare da wani hakki na mutane ko hukumomi ba.
A yayin ganawarsa da tawagar shugabannin addinin Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau a fadar gwamnati ranar Alhamis, Tinubu ya danganta nasarar zaɓen da ya samu da sa hannun Ubangiji, da tsare-tsare da kuma goyon bayan ƴan Najeriya.
“Babu wasu mutane da ke juya gwamnatina da ake kira da ‘cabal’. Ba ni da waɗanda suka tallafa min ko kuma ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓe na, duk wani kuɗi da aka kashe lokacin yaƙin zaɓena daga aljihuna suka fito, a wasu lokutan ma, irin ƙalubalen da na fuskanta a lokacin sai a hankali, amma Allah Madaukakin Sarki ya riga ya ce ni zan zama shugaban Nigeriya.” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma jaddada bukatar mayar da hankali kan makomar ƴan kasar, inda ya ce, “Abin da ya kamata ya mu sanya a zukatanmu shi ne makomar ƴaƴanmu. Muna da abubuwa da yawa da za mu koya musu a kan abin da ake bukata don zama ɗan ƙasa nagari.”


