Magajin garin Mariupol na ƙasar Ukraine, Vadym Boichenko, ya fitar da sanarwa bayan bayyana tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukrain a kan brinin nasa.
Ya ce, “Mariupol ba tituna ba ne kawai da gidaje,” a cewarsa. “Mutanensa ne.”
Ya ƙara da cewa: “Sakamakon ruwan wuta ba ƙaƙƙautawa daga ‘yan kama-wuri-zauna, babu wani zaɓi illa mu bai wa mazauna garin damar tserewa daga Mariupol.”
Tsagaita wutar da Rasha ta yi na ɗan lokaci ne a safiyar Asabar ɗin nan, domin bai wa fararen hula damar guduwa.