Fadar shugaban kasa, ta ce babu wani sashe na sabon ƙudurin haraji da ta gabatar ga majalisa domin samun amincewa da ya tanadi soke wasu hukumomi irin su TETFUND, da NASENI, da kuma NITDA.
Haka kuma ta ce ƙudurin kamar yadda ake ta yaɗa maganganu ko alama ba zai jefa yankin Arewacin ƙasar cikin talauci ba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyaa haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.
Tun bayan da jam’a suka fara muhawara a kan ƙudurin a ‘yan makonnin da suka gabata, ‘yan siyasa da sauran masu sharhi na ta ɓoye gaskiya a kan ƙudurin, inda ya ce da gangan suke yaɗa ƙarerayi da kawara da jama’a daga fahimtar gaskiya a kan lamarin.
Ya ce yawancin maganganun da ake yi na suka a kan ƙudurin ba ana yin su ne bisa wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, illa shaci faɗi kawai.
Onanuga ya ce yayin da wasu masu sharhin suka yi ƙoƙarin haifar da saɓani tsakanin jama’a da ‘yan majalisar dokoki, wasu kuma sun raba kan ƙasar ne tsakanin wani sashe da wani.
Kakakin ya ce ko alama wannan ƙuduri ba zai azurta jihar Lagos ko Ribas, ya kuma sa wasu sassan ƙasar su ƙara talaucewa ba kamar yadda ake yayatawa ba.
Ya ce saɓanin wannan zargin ƙudurin zai taimaka ne wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman ma masu ƙaramin ƙarfi.