Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta karyata sakonnin da ke cewa wasu ‘yan bindiga suna shirin kai hare-hare a Zaria.
Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar ranar Laraba ya nemi mutanen birnin na Zaria da su yi watsi da sakonnin yana mai cewa ba su da kanshin gaskiya.
“An jawo hankalin gwamnatin Kaduna kan wani sako da ake watsawa sosai da ke bai wa mutane shawarar cewa su guji shiga ko fita daga Zaria, wanda ke zargin cewa akwai daruruwan ‘yan bindiga a yankin Dumbi da Jaji a kan hanyar Zaria. Gwamnatin Jihar Kaduna tana mai karyata wannan sako. kuma tana umartar mutane su yi watsi da shi baki daya,” a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa ana yada sakon ne domin a tayar da hankulan jama’a, tana mai tabbatar wa mazauna yankin da matafiya cewa babu wata matsala a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria. In ji BBC.