Rundunar ‘yan sanda da kasa, ta musanta jita-jitar da ake yadawa a Kano game da harin da aka kai shelkwatar ‘yan sandan Najeriya shiyya ta daya a jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na shiyyar a Kano, SP Abubakar Zayyanu Ambursa ya tabbatar wa wakilin NIGERIA TRACKER faruwar lamarin.
Ya ce, yana cikin ofishin da wuri kuma ko bayan Sallar Juma’a na Sa’a guda da suka yi a Masallacin Zone 1 ba a kai wani hari ba.
Da ya samu labarin haka sai ya fita ya sa ido a kan jami’an ‘yan sandan da ke aikin kofar shiga bayan Sallar Juma’a kuma abin da suke yi shi ne duban ababen hawa da aka saba yi da sauran tsare-tsare na tsaro bayan Sallar Juma’a.
Ya kuma bukaci jama’a da kada su firgita kuma su kwantar da hankalinsu, domin babu wani hari da aka kai yankin.