Ƴan Matan da hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama a wani samame da ta yi a gidajen shaƙatawa a jihar, sun bayyana cewa ƴawan baɗala ba shi da wani daɗi saia dai zubar da mutuncinnsu.
Ƴan Matan sun bayyana hakan ne a shalƙwatar hukumar dake Sharada a jihar.
Sun ce tabbas wannan kaman na su abun nadama ne a don haka suke gargaɗin sauran ƴan Mata su shiga taitayin su tare da ganin sun zauna a gaban iyayen su ko kuma su yi aure.
Wasu daga cikin ƴan matan an gwada su inda hukumar ta tabbatar da su na ɗauke da cutaai karya garkuwar jiki.