fidelitybank

Babu wani cin hanci da muka karba – PDP

Date:

Kwamitin gudanarwar babbar jam’iyyar hamayya na PDP, ya musanta rahotonni da ke cewa an bai wa wasu manyan jagororin jam’iyyar cin hanci.

Kwamitin ya ce, kudaden alawus din gidaje ne wanda aka aiwatar bisa tsarin doka, ba cin hanci ba ne kamar yadda ake zargi.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Debo Ologunagba ya fitar ranar Talata bayan kammala taron kwamitin zartarwar jam’iyyar a Abuja babban birnin kasar.

Ologunagba ya ce, a zaman da kwamitin ya yi, ya yi duba game da labarin da wata jarida a kasar ta buga, tana mai cewa kudin alawus din gidaje da aka biya manyan jagororin jam’iyyar kudi ne na cin hanci.

“Bayan bincike da kwamitin ya gudanar a zamansa, ya fahimci cewa kudin ba cin hanci ba, kudin alawus din gidaje ne,” in ji shi.

Ologunagba ya ce jam’iyyar ta kafa kwamiti tare da ba shi wa’adin mako guda domin duba lamarin tare da mika rahotonsa ga kwamitin gudanarwar jam’iyyar domin daukar mataki na gaba.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...

Daga yau wankin koda a Najeriya ya koma dubu 12 maimakon dubu 50 – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da rage farashin...
X whatsapp