fidelitybank

Babu wanda ya tuntube mu akan shiga jam’iyyar APC – NNPP

Date:

Jam’iyyar hamayya ta NNPP a Kano ta ce, kawo yanzu babu wanda ya tuntubeta game da shiga jam’iyyar APC.

Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf, ya shaidawa BBC cewa wannan kira da shugaban APC ya yi musu a kwararo suka ji shi.

”Mun ji bayyanin cewa ya miko wannan Æ™oÆ™on bara na gwamna ya dawo jam’iyyar APC to amma abin mamaki shi ne, shi Ganduje a matsayinsa na tsohon gwamna da tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake isarwa gwamna mai ci sako idan ana son ya je wurinsa”, in ji Sanusi.

Ya kuma kara cewa gwamna Yusuf ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko kin barin jam’iyyarsa.

”Amma maganar da muka ji ya faÉ—a a kafafen yaÉ—a labarai na zumunta mu ka ji ta kuma a nan mu ka barta’’

”Ka san ita siyasa ko in ce sauya sheka ta siyasa kamar canza gida ne, ba ka tashi lokaci É—aya kawai ka dauki jakarka ka fita, ka ce wai ka canja gida.

“Akwai abubuwan da za ka iya yi kafin ka ce ka canja gida saboda don haka mu a wurinmu wannan sako mun ji ne kawai kamar a sama”, in ji shi.

Wannan yunkuri na jam’iyyar APC na zuwa ne bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, na cewa É“angarorin biyu su je su sasanta da juna.

Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp